Wayyo abin tausayi: Wani Mutum ya mutu bayan ya ciro Naira N100,200 daga banki
- Direban motar yana ta tambayar fasinjan kudin motarsa amma yayi shiru, ashe ya mutu
- Yanzu haka an tsare motar direban don cigaba da bincike kafin yan uwansa su zo
Hayaniya da hargowa sun barke a tashar mota dake yankin Ojota na Jihar Lagos, sakamakon mutuwar wani fasinja a cikin motar haya. Mutumin dai an bayyana sunansa a matsayin Muyibi, kuma ya mutu ne bayan da ciro kudinsa har fiye da dubu dari a reshen bankin UBA na Ojota a Jihar dake Lagos.
Direban dai ya bukaci da fasinjan ya ba shi kudinsa amma shiru bai ko motsa ba balle ya amma masa. Kamar yadda jaridar Punch ta rawaito.
Direban motar kawai sai yayi ta tafiya sauran mutane na sauka a wurare daban-daban, inda shi kuma mamacin ya lafke an zata bacci yake, har sai da aka karasa tasha inda kowa anan dole zai sauka, tsayawarsu ke da wuya sai direban ya kuma.
KU KARANTA: Jagaliyar siyasa: an kaiwa wani masoyin Buhari, mai caccakar Tambuwal hari a wurin biki
“Shirun da mamacin yayi ne ya sa direban taba shi domin ya tashe shi daga baccin, amma sai ya ji jikinsa yayi sanyi, nan take direban ya nemi da akawo masa agaji domin duba fasinjan nasa, bayan mutane sun duba shi ne suka gano cewa ya sheka barzahu.” Kamar yadda wasu dake wurin suka shaidawa majiyarmu.
Yan sandan yankin Ogudu sun tabbatar da faruwar al’amarin, harma suka jajantawa direban motar da fasinjan ya mutu a motarsa domin kuwa duk da cewa ba’a tsare shi ba; amma an tsare motarsa har sai lokacin da yan uwan mamacin zasu bayyana.
Kakakin yandan Jihar SP Chike Oti ya bayyana cewa, sun samu gawar mamacin tare da kudaden nasa da ya ciro daga banki har Naira dubu dari da nai dari biyu (N100,200) a cikin jakarsa tare kuma wayarsa ta salula amma sai dai layin cikinta sabo ne babu lambar waya a ciki balle su kira.
Wakilinmu ya gaza samun damar magana da shugaban direbobin na yankin da abin ya faru, a yayin rubuta wannan rahoto.
Amma sai dai wata majiya daga tashar ta bayyana cewa lallai lamarin ya faru da misalign karfe 3 p.m ranar Juma’a.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng