Jagaliyar siyasa: an kaiwa wani masoyin Buhari, mai caccakar Tambuwal hari a wurin biki

Jagaliyar siyasa: an kaiwa wani masoyin Buhari, mai caccakar Tambuwal hari a wurin biki

- Yan jagaliyar siyasa sun kaiwa wani masoyin Buhari kuma jigo a jam'iyyar APC hari a Sokoto

- Da kyar yan sanda sukai nasarar kwatarsa a hannun yan jagaliyar

- Bayan samun kansa, yayi kira ga mutanen Sokoto su zo su hadu domin tubuke Tambuwal daga gwamna

Wasu matasa da ake kyautata zaton yan jagaliyar siyasa ne, sun kai hari ga Alhaji Dahiru Yabo, mai yawan caccakar gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal.

Alhaji Dahiru dai jigo ne a jam’iyyar APC a jihar ta sokoto, kuma shahada'un shugaba Muhammadu Buhari ne, ya bayyana cewa, an kai masa harin ne a hanyarsa ta fita daga harabar wurin daurin auren yan uwar gwamnan jihar da ya halarta.

Kuma ya kara da cewa, tabbas wannan harin wani yunkuri ne dake nuni da yadda wasu mutane ke farautar rayuwarsa domin kashe shi, alhali lokacinsa bai yi ba sakamakon ra’ayin da yake da shi a siyasance.

Jagaliyar siyasa: an kaiwa wani mai caccakar Tambuwal hari a wurin biki
Alhaji Dahiru Yabo

Wasu da abin ya faru a gaban idonsu, sun bayyana cewa, har sai da jamia’an tsaro suka shiga tsakani sanan suka dakatar da yan jagaliyar.

Harin da aka kai min jiya, ya nuna a fili yadda wasu suke da burin ganin karshe na sakamakon karin fahimta. Saboda da haka ya kamata ga duk masu son cigaban jihar Sokoto da su zo mu tabbatar mun fitar da wannan gwamnan daga gidan gwamnati a saboda rashin iya shugabanci da kuma rashin kawo cigaba ga mutanen Sokoto.” A cewar Alhaji Dahiru.

KU KARANTA: In dai kuna yin wadannan abubuwan, to ba sai kaje asibiti ganin likita ba

Jam’iyyar APC dai na fama da rikice-rikicen cikin gida a jihar ta Sokoto, wanda haka yake barazana ga hadin kan jam’iyyar.

Rikici dai tsakanin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal da tsohon Sanata Umaru Dahiru rikici ne da ya kusa daidaita jam’iyyar a jihar.

Jagaliyar siyasa: an kaiwa wani mai caccakar Tambuwal hari a wurin biki
Jagaliyar siyasa: an kaiwa wani mai caccakar Tambuwal hari a wurin biki

Rikicin ya samo asali ne bayan da Tambuwal din ya samu nasara a zaben cikin gida kafin zaben 2015. Sanata Dahiru ya dai kalubalanci Tambuwal din a kotu har sau biyu kafin daga bisani a shawo kansa da ya hakura da daukaka kara zuwa kotun koli.

Bayan sulhu da akai tsakaninsu, yanzu haka suna iya zama wuri daya har ma su tattauna, kuma tsohon sanatan ya halarci daurin auren yar uwar gwamnan jihar.

Tun bayan sulhun ne kuma tsohon Sanatan yake goyon bayan gwamnan tare da yabawa irin akace –aikacen da yake yi.

Majiyarmu dai ba ta samu wata amsa daga kakakin rundunar yan sanda ta jihar ta Sokoto ba, DSP Cordelia Nwawe, sakamakon rashin samunta a waya.

Duk yunkurin da majiyar ta mu tayi don samun Gwamna Tambuwal ko Sanatan ko kuma shugabancin jam’iyyar ta APC su ce wani abu, ya ci tura, amma shugabancin jam’iyyar ya ce zai yi magana akan batun idan lokaci yayi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng