Su waye zasu kara da Buhari a 2019: Saura dai wata 10 zabukan, na cikin gida wata 4

Su waye zasu kara da Buhari a 2019: Saura dai wata 10 zabukan, na cikin gida wata 4

- An kusa shiga zabukan 2019 a Najeriya

- A cikin gida a APC Saraki zai iya takara

- A waje akwai irinu Atiku Abubakar

Su waye zasu kara da Buhari a 2019: Saura dai wata 10 zabukan, na cikin gida wata 4
Su waye zasu kara da Buhari a 2019: Saura dai wata 10 zabukan, na cikin gida wata 4

Zabukan cikin gida na APC dai za'a yi su ne bayan babbar Sallah, kamar watan Agusta zuwa Octoba kenan, inda ake sa rai shugaba Buhari zai kayar da Bukola Saraki da ko Rabiu Kwankwaso wanda niyyar fitowa takara a cikin gida.

Daga nan sai ya kara da na manyan jam'iyyu a Fabrairun badi inda rai. Ana hasashen zai kara da Ko Atiku Abubakar a PDP ko Sule Lamido, ko duk su biyun a jam'iyyu mabambanta, musamman jam'iyyar SDP ta tsohon dan takara MKO Abiola.

Kodayake Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari bai fito fili ya bayyana aniyyarsa ta sake tsayawa takara a zaben 2019 ba, amma na kusa da shi sun sha bayyana cewa babu abin da zai hana shi yin tazarce.

DUBA WANNAN: Kisan GIlla a Offa na jiya: Yadda suka kitsa harin

Daga kudu dai ba'a tsammanin akwai wani dan hamayya da za'a samu mai kwari, indai ba Donald Duke ko Uzor KAlu ba, manyan tsofin gwamnoni da basu mayar da mayatarsu ba.

Sai kuma Ayodele Fayose, wanda ake gani wasu cikin na arewa zasu dauka domin raka tikiti.

A gefe daya kuma, ana sa rai Obasanjo zai karfafa wanda yake tsammani zai iya kayar masa da Buharin da ma dakile masa tsohon abokin gaba Atiku Abubakar, musamman Sule Lamido ko Rabiu Kwankwaso

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng