Rundunar soji sun ragargaji yan Boko Haram 5 a Adamawa
Rundunar sojin operation LAFIYA DOLE sun ragargaji wasu yan ta’addan Boko Haram a jihar Adamawa, yankin Arewa maso gabashin Najeriya.
Wannan na faruwa ne bayan hukumar ya alanta hallaka yan bindiga 21 a jihar Zamfara a farkon wannan makon.
Kakakin hukumar sojin, Texas Chukwu, ya bayyana wannan ne a yau Asabar, 7 ga watan Afrilu a shafin ra’ayi da sada zumuntar hukumar.
Yace: “Rundunar sojin operation LAFIYA DOLE a ranan 6 ga watan Afrilu sun ragargaji wasu yan ta’addan Boko Haram a Barkin Dutse, jihar Adamawa, bisa rahoton wasu mafarauta.
Yan ta’ddan yayinda suka hango jami’an soji suka bude musu wuta. An hallaka yan Boko Haram 5 yayinda wasu suka arce. Daya daga mafarautan ya rasa rayuwarsa.
An kwato bindigan AK47 guda 5, carbin harsasi 5 da kuma wasu makamai na musamman.”
KU KARANTA: Iyalan Gwamna Yahaya Bello sun tsallake rijiya da baya
Legit.ng ta kawo muku rahotannin cewa shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan takardan baiwa hukumar soji $1bn domin sayen makamai da kawar da Boko Haram.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng