Jerin sunayen barayi: FG za ta sakin sabbin sunaye, wannan zai kunshi tsaffin gwamnoni, ministoci da ma’aikatan banki

Jerin sunayen barayi: FG za ta sakin sabbin sunaye, wannan zai kunshi tsaffin gwamnoni, ministoci da ma’aikatan banki

Yayinda ake cece-kuce kan sunayen barayin kudin gwamnati da minister yada labarai da al’adu ya saki kwanakin nan, akwai alamun cewa gwamnati zata sake sakin sabbin sunaye domin bayyanawa yan Najeriya wadanda suka jefa mu cikin halin da muke ciki.

Rahotanni sun bayyana cewa wannan sabon jerin zai kunshi sunayen wadanda ma basu riga sun gurfana gaban kotu ba tukun.

Kana wannan jerin zai kunshi sunayen gwamnoni, ministoci da kuma wasu ma’aikatan gwamnati.

Ministan labarai da al’ada, Alhaji Lai Mohammed, ya saki sunayen mutane 55 wadanda suka sace N1.34tn karkashin gwamnatin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.

Jerin sunayen barayi: FG za ta sakin sabbin sunaye, wannan zai kunshi tsaffin gwamnoni, ministoci da ma’aikatan banki
Jerin sunayen barayi: FG za ta sakin sabbin sunaye, wannan zai kunshi tsaffin gwamnoni, ministoci da ma’aikatan banki

Amma maganan da masu sharhi kan al’amuran yau da kullum sun ce anyi son kai wajen sakin sunayen saboda sunayen yan jam’iyyar adawa ta PDP kawai aka saki alhali akwai yan jam’iyyar APC da sukayi sata.

KU KARANTA: Kwandasta yayi lalata da 'yar 11, har ta fara yoyon fitsari

Amma wata majiya daga fadar shugaban kasa wanda aka sakaye sunansa ya bayyanawa manema labarai cewa wannan sabon jeri da za’a saki zai kunshi wadanda suka amsa kudi daga hannun Sambo Dasuki da kuma FG gabanin zaben 2015.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng