Na mu ya samu: Buhari zai shimfida bututun man fetur da iskar gas zuwa arewa
Mahukunta a hukumar nan dake kula da kamfanonin albarkatun man fetur na NNPC mallakin gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari sun sanar da bayar da kwangilar shimfida bututan mai har biyu zuwa Arewa.
Wadannan bututan man dai kamar yadda muka samu za su farfado da masana'antu da kuma tattalin arzikin arewacin kasar nan idan har aka kammala su.
KU KARANTA: Zaben 2019: Ko Buhari fito ko mu kai shi kotu - Ganduje
Legit.ng ta samu cewa daya daga cikin kwangilolin da aka bayar shine na shimfida bututun iskar gas mai tsawon kilomita akalla 200 wanda zai taso daga garin Ajaokuta na jihar Kogi zuwa Kaduna sannan ya wuce zuwa Kano.
Dayar kwangilar kuma kamar dai yadda muka samu ita kuma ta kunshi shimfida karin kilomita 221 ta bututun da zai tashi ne daga jihar Kaduna zuwa Kano.
A wani labarin kuma, Gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta sanar da amincewar ta a kan gina sabuwar matatar mai da iskar gas watau Liquefied Petroleum Gas extraction plant (LPG) a takaice a jihar Ribas dake a kudu maso kudancin Najeriya nan ba da dadewa ba.
Bangaren dake kula da albarkatun man fetur da iskar gas na kasar ne dai ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a garin Abuja.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng