Ka kyale hukumar INEC ka fuskanci gwamnatinka – Wata Kungiya ga Wike
- Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike ya dade yana maganganu akan hukumar zabe mai zaman kanta (INEC)
- Wannan ya jawo hankalin kungiya mai zaman kanta ta wayayyu mai suna Citizen for Democratic Governance
- Kungiyar ta cewa gwamnan ya mayar da hankalinsa akan aikinsa na Gwamnan jihar Rivers ya kyale hukumar INEC ta gudanar da nata aikin
Kungiya mai zaman kanta ta wayayyu mai suna Citizen for Democratic Governance, ta bukaci gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike, da ya mayar da hankalinsa akan aikinsa na gwamnan jihar Rivers ya bar hukumar zaben mai zaman kanta ta INEC tayi aikintana zaben 2019.
Kungiyar ta nuna damuwarta akan abunda gwamnan yake kokarinyi na lalata tabbashin da hukumar take bayarwa game da zaben 2019.
A jawabin da mai kula da shirye shirye na tarayya Anthony Osagbemi ya turawa Legit.ng, yace gwamnan ya dade yana maganganu marasa amfani akan zaben 2019 ba tare da yanada wata kwakwarar shaida ba.
KU KARANTA KUMA: Matasan kudu maso arewa sunyi jinjina ga Buhari akan cigaban da ya kawo
Osagbemi yace ciyaman na hukumar zaben mai zaman kanta yace kuri’u da aka kidaya a gabansa ne za’ayi amfani dasu, wannan ke nuna cewa zabe nata kara samun cigaba a jihohi da aka gudanar dasu a fadin Najeriya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng