Dandalin Kannywood: Abunda na sa gaba bayan daina fitowa a fim – Sadiya Gyale

Dandalin Kannywood: Abunda na sa gaba bayan daina fitowa a fim – Sadiya Gyale

Shahararriyar jarumar nan ta Kannywood wacce aka dama da ita a lokutan baya, Sadiya Muhammad Gyale ta yi tsokaci akan abunda ta sa a gaba bayan barinta masana’antar ta shirya fina-finai.

A cewar jarumar ta kama sana’a ne gadan-gadan, inda ta ke saida kayayyaki daban-daban.

Sadiya tace tana saida kayan mata, na maza dama kayan noma domin tafiyar da al’amuranta na yau da kullun.

Dandalin Kannywood: Abunda na sa gaba bayan daina fitowa a fim – Sadiya Gyale
Dandalin Kannywood: Abunda na sa gaba bayan daina fitowa a fim – Sadiya Gyale

Jarumar ta bayyana hakan ne a wani hira da tayi da jaridar Leadership Hausa.

KU KARANTA KUMA: Fadar shugaban kasa ta kare Buhari akan amincewa da bayar da $1bn na tsaro

Da aka tambayeta kan batun aure, kyakyawar jarumar tace Insha Allah suna ta addu’a, Allah Ya kawo miji nagari mafi alheri.

A baya Legit.ng ta kawo cewa tsohon mijin shahararriyar jarumar nan ta Kannywood, Sadiya Gyale wato Alhaji Abubakar Muhammad ya amsa kiran mahallicin sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng