Abun sirri ne: Ko me shugaba Buhari zai sake zuwa yi Landan?
Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya ta Peoples Democratic Party, PDP tare da sauran magoya bayan ta sun bayyana shakkun su game da abunda suka kira dodoridon da fadar shugaban kasa ke yi wa 'yan Najeriya musamman ma game da tafiyar da yake shirin yi zuwa birnin Landan sati mai zuwa.
Haka ma dai jam'iyyar ta bukaci samun sahihin bayani game da lafiyar ta shugaban kasa da cikkanen abunda zai je yi tare da kuma adadin kudin kasa da zai kashe yayin tafiyar ta sa.
KU KARANTA: Gwamnoni 5 da ke fuskantar barzanar shan kasa a 2019
Legit.ng ta samu cewa wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da jami'in yada labarai na jam'iyyar ta Peoples Democratic Party, PDP Mista Kola Ologbondiyan ya fitar a Abuja.
A wani labarin kuma, Da alama dai rikicin dake a ta faruwa a tsakanin 'ya'yan jam'iyyar All Progressives Congress, APC mai mulki a Najeriya bai da alamun karewa musamman ma dai bisa dalilin wa'adin shugabannin jam'iyyar a dukkan matakai.
Wannan dai kamar yadda muka samu na faruwa ne biyo bayan kiran da daya daga jigogin jam'iyyar dake a jihar Bayelsa ta shiyyar kudu maso kudancin kasar mai suna Perekeme Kpodo da yayi na cewa ya kamata shugaban jam'iyyar na yanzu Cif Oyegun ya sauka daga kan mukamin sa cikin ruwan sanyi.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng