Faruwar wasu ababe 3 a watan Maris da suka tashi hankalin dandalan sada zumunta

Faruwar wasu ababe 3 a watan Maris da suka tashi hankalin dandalan sada zumunta

Watan Maris da ya gabata wata ne mai cike da faruwar ababe kama daga ababen farin ciki, ban mamaki da kuma al'ajabi. A sakamakon haka Legit.ng da sanadin jaridar Daily Trust ta kawo muku jerin ababe 3 da suka faru kuma suka janyo a kai ta musayar yawu a dandalan sada zumunta.

1. Sako 'yan matan Dapchi:

'Yan Matan Dapchi yayin ziyarar shugaba Buhari a fadar sa
'Yan Matan Dapchi yayin ziyarar shugaba Buhari a fadar sa

Farin cikin sakar 'yan matan Dapchi 101 da 'yan ta'addan Boko Haram suka yashe a makarantar su dake garin Dapchi a jihar Yobe ta janyo abin magana da musayar yawu a dandalan sada zumunta.

2. Fallasa ainihin albashin 'yan majalisar Dattawa da Sanata Shehu Sani yayi:

Sanata Shehu Sani
Sanata Shehu Sani

Wannan labari ya jefa mutane da dama a kasar nan cikin mamaki yayin da Sanata mai wakiltar jihar Kaduna ta tsakiya ya fashe tulun da ya dade da sakaya albashin 'yan majalisar dattawan kasar nan.

KARANTA KUMA: Nau'ikan abinci 10 dake kawar da warin jiki su kamsasa shi

Sanatan dai ya bayyana cewa, akalla kowane Sanata yana samun alawus na N13.5m a kowane wata wanda wannan doriya ne akan albashin su na kimanin N750, 000 a kowane watan duniya.

3. Furucin T. Y Danjuma na kowa ya kare kan sa a kasar nan:

T. Y Danjuma
T. Y Danjuma

Batun tsohon ministan tsaro Janar T. Y Danjuma, da ya bayyana a watan da ya gabata na cewar kowane dan Najeriya ya tashi tsaye domin kare kan sa a sakamakon hare-haren da makiyaya ke kaiwa a yankuna daban-daban ya janyo cecekuce a dandalan sada zumunta.

A yayin da wasu suka goyi bayan wannan batun na tsohon Sojan, wasu ko ba su da ta cewa face suka a gare shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel