Ba lafiya: Hotunan mata masu juna-biyu 200 suna gudanar da zanga-zanga a Najeriya

Ba lafiya: Hotunan mata masu juna-biyu 200 suna gudanar da zanga-zanga a Najeriya

Jama'ar gari sun dan shiga cikin rudani biyo bayan wata zanga-zangar lumana da mata masu ciki su kimanin 200 suka yi a garin Akure, babban birnin jihar Ondo a ranar Alhamis 5 ga watan Afrilu.

Majiyar mu dai ta shaida mana cewa daruruwan matan dai an gan su kowace da ciki niki-niki suna ta faman kwankwami da cancakwato yayin da kuma suka tare hanyar shiga da fita na asibitin kwararrun garin na Akure.

Ba lafiya: Hotunan mata masu juna-biyu 200 suna gudanar da zanga-zanga a Najeriya
Ba lafiya: Hotunan mata masu juna-biyu 200 suna gudanar da zanga-zanga a Najeriya

KU KARANTA: Amarya tayi ba-zata a garin Bauchi

Legit.ng ta samu cewa babban musabbabin yin zanga-zangar ta su dai ba za ta rasa nasaba ba da abunda suka kira rashin adalcin da gwamnati tayi masu na karin kudin ansar haihuwa zuwa Naira dubu 25 da kuma Naira dubu 50.

A wani labarin kuma, A wani mataki mai cike da karsashi da Allah-san-barka, wata amarya diyar daya daga cikin manyan manajojin kamfanin albarkatun man fetur na NNPC mai suna Aisha Bala-Wunti ta zabi baiwa marasa lafiya musamman ma marasa galihu kiwon lafiya kyauta a bikin ta maimakon shagulgula.

Da take karin haske game da shirin, amaryar ta bayyana cewa an dauko tawagar likitocin ne daga kasar Indiya kuma kwararri ne a dukkan fannonin kiwon lafiya musamman ma a matakin farko.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng