An kama wani kato da ya boye 'yan mata 4 yana lalata da su a Arewa

An kama wani kato da ya boye 'yan mata 4 yana lalata da su a Arewa

Kungiyar 'yan banga reshen jihar Kebbi dake a shiyyar arewa maso yammacin Najeriya sun samu nasarar cafke wani kato mai suna Abdul-Aziz Muhammad Jega dan kimanin shekaru 35 a duniya wanda ya boye wasu kananan yara 'yan mata su hudu 'yan shekaru 8 zuwa 12 yana kwanciya da su.

'Yan bangar dai kamar yadda muka samu tuni har sun mika mutumin zuwa ga jami'an hukumar hisbah ta jihar domin gurfanarwa a gaban kotu.

An kama wani kato da ya boye 'yan mata 4 yana lalata da su a Arewa
An kama wani kato da ya boye 'yan mata 4 yana lalata da su a Arewa

KU KARANTA: Yan fashi na balle bankuna a jihar Kwara

Legit.ng ta samu cewa da yake amsa tambayoyi daga jam'ian Hisba, shi Abdul-Aziz din ya ansa laifin sa yayin da kuma ya nuna matukar nadamar sa tare da yinyar karbi laifinsa na boye kananan yara alkawarin ba zai karaba.

A wani labarin kuma, Jama'ar gari sun dan shiga cikin rudani biyo bayan wata zanga-zangar lumana da mata masu ciki su kimanin 200 suka yi a garin Akure, babban birnin jihar Ondo a ranar Alhamis 5 ga watan Afrilu.

Majiyar mu dai ta shaida mana cewa daruruwan matan dai an gan su kowace da ciki niki-niki suna ta faman kwankwami da cancakwato yayin da kuma suka tare hanyar shiga da fita na asibitin kwararrun garin na Akure.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng