Nigerian news All categories All tags
An rufe fiye da Masallatai da Coci 6000 a kasar Rwanda sakamakon rashin hali na kula da su

An rufe fiye da Masallatai da Coci 6000 a kasar Rwanda sakamakon rashin hali na kula da su

Gwamnatin kasar Rwanda ta rufe dubunnan Coci da masallatai da dama a yayin da take fafutikar ta na yin ruwa da tsaki akan wuraren gudanar da ibadu da hukumomi suka bayyana cewa suna tafka barazana ga rayuwar mabiya addinan.

Shugaban kasar Rwanda; Paul Kagame

Shugaban kasar Rwanda; Paul Kagame

A watan Maris din da ya gabata ne shugaban kasar Rwanda Paul Kagame, ya bayyana cewa yana mamakin yadda adadin wuraren ibadu suka yawaita a wannan karamar kasa ta su dake yankin Gabashin Afirka.

Kagame yake cewa, Kasar Rwanda ba ta da bukatar yawan wuraren ibadu, inda yace ana bukatar yawaitar su ne a manyan kasashe masu babban ci gaba ta fuskar tattalin arziki da zai iya kulawa da kuma dawainiya da su.

Sai dai wannan rufe wuraren ibadu ya janyo cecekuce a kasar yayin da wasu ke ganin an dakile musu 'yancin su da kundin tsari ya bayar da dama domin kowa ya bi ra'ayin ta fuskar addini.

Rahotanni sun bayyana cewa, a halin yanzu gwamnatin kasar ta garkame wasu masu tayar da jijiyoyin kan wannan lamari da gwamnatin kasar ke ganin su na neman tayar da zaune tsaye.

A yayin haka kuma, gwamnatin kasar ta bayar da dalilin ta na yanke wannan danyen hukunci da cewa, mafi akasarin wuraren addinan su na da nakasun ingatattun gine-gine da rashin aminci wanda ke yiwa mabiya addinan barazana ga lafiya da kuma rayuwar su.

KARANTA KUMA: Kungiyar Musulman Lauyoyi ta ki amincewa da sabuwar dokar Kotu kan tsarin sanya Tufafi

Wannan dalili da gwamnatin ta gindaya ya samu goyon bayan na mafi akasarin shugabannin addinan da cewar ko shakka ba bu dole gwamnatin ta kare lafiyar al'umma ta ta kowane da ta ga ya dace.

Legit.ng ta fahimci cewa, a watan Maris din da ta gabata ne wasu mabiya 16 na addinin Kirista suka rasa rayukan su yayin da kimanin 140 suka samu muggan raunuka a sakamakon kwarankwatsa da ta fadowa ginin mai nakasun ginin zamani da zai tsotse wannan tsautsayi na walkiya.

Kafofin watsa labarai na kasar sun bayyana cewa, a halin da gwamnatin Kagame ta garkame sama da Coci 6000 yayin da kuma ta bame kimanin masallatai 100 a fadin kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel