Shari’a sabanin hankali: An yanke ma barawon sigari da kwalaben giya hukuncin kisa

Shari’a sabanin hankali: An yanke ma barawon sigari da kwalaben giya hukuncin kisa

Wani Alkalin babbar kotun jihar Ekiti dake zamanta a garin Ado-Ekiti ya yanke ma wani mutumi mai suna Raji Babatunde hukuncin kisa bisa kama shi da laifin satar kwalin sigari, Rothmans da kwalaben giya guda bakwai.

Legit.ng ta ruwaito Alkalin mai shari’a Cornelius Akintayo ya bayyana cewa ya kama Babatunde da laifin mallakar makami ba tare da ka’ida ba da kuma aikata laifin fashi da makami.

KU KARANTA: Wata Mata ta hau dokin zuciya, ta yi sibarnabayyen wata jaririya yar wata 8

Shi dai Babatunde ya kasance dan wata kungiyar yan fashi da makami da suka kai samame wani gida mai lamba 15, titin Odundun a unguwar Okesa, da gida mai lamba 5c dake titin Dallimore, dukkaninsu a cikin garnin Ado Ekiti.

Alkalin yace yan fashin sun yi ma wani Alhaji Bello Mudashiru fashin wayoyinsa guda biyu, samfurin Nokia da Tecno, sa’annan suka yi ma wani Femi Oladele fashin kwalin sigari, da kwalaben giya guda bakwai, inda sauran yan fashin suka tsere, amma aka kama Babatunde, daga bisani kuma aka kama Sunday.

A yayin zaman Kotun na farko daya gudana a shekarar 2016, 1 ga watan Feburairu, Babatunde da Sunday sun musanta tuhume tuhumen da ake yi musu, bayan Yansanda sun gabatar da hujjoji ga Kotu da suka hada da bayanin amsa laifin daga mutanen, adduna hudu, wuka, kwalbar giya Trophy, fasashshiyar kwalbar giyan Star, rediyo da hula hana sallah.

A nasa bangaren, Babatunde ya gabatar da mahaifiyarsa a matsayin shaidar sa, wanda ya bayyana ma Kotu cewar yaronta na kan hanyar dawowa ne daga Coci a daren da Yansanda suka kama shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel