Nigerian news All categories All tags
Makiyaya sun hallaka manoma 2 tare da raunata wasu 3

Makiyaya sun hallaka manoma 2 tare da raunata wasu 3

Rahotanni sun kawo cewa makiyaya sun hallka mutane biyu a garin Agasha, karamar hukumar Guma dake jihar Benue.

Makiyayan sun kuma harbi mutane uku wanda a yanzu haka suna karban magani a wani asibiti da ba’a bayyana ba sannan kuma suka sace daruruwan shanaye.

Kakakin yan sanda DSP Moses Yamu yace bai samu labara daga sashin yan sandan Guma ba tukuna.

Shugaban kungiyar TIV, Cif Aondona Adzuu ya fadama jaridar The Nation cewa makiyayan sun kai farmaki gidan wanda abun ya shafa Asema da misalign karfe biyu na tsakar dare lokacin da kwa yayi bacci.

Makiyaya sun hallaka manoma 2 tare da raunata wasu 3

Makiyaya sun hallaka manoma 2 tare da raunata wasu 3

“Sun mamaye gidansa dake hanyar gonar Tilley Gyado a garin Agasha sannan suka harbe shi har lahira kafin suka sace shanaye 100,” inji Cif Adzuu.

KU KARAN TA KUMA: Zogala: Maganin dake kashe cutar daji ya kuma hana cutar siga

Yayinda suke tserewa sun hari mutane uku wadanda ke karban magani a wani asibiti.

Adzuu wanda ya kasance shugaban Agasha ya bayyana cewa mutun na biyun ya mutu sakamakon harbi da ya samu daga maharan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel