Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Sarkin Anka, Alhaji Attahiru Ahmad
Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi sarkin Anka kuma shugaban majalisan sarakunan gargajiyan jihar Zamfara, Alhaji Attahiru Ahmad, a daren jiya Laraba, 4 ga watan Afrilu, 2018 a fadar shugaban kasa, Aso Vila Abuja.
Sarkin ya isa fadar shugaban kasa ne tare da gwamnan jihar Zamfara, Abdul Aziz Yari inda skayi ganawa ta musamman.
Ana kyautata zaton cewa sun tattauna kan al’amuran da suka shafi tsaro a jihar Zamfara musamman a karamar hukumar Anka inda yan bindiga ke ta’asa a kwanakin nan.
Zaku tuna cewa ranan Alhamis da ya gabata, yan bindigan sun kai mumunan hari kan al’ummar Bawar Daji inda suka hallaka rayukan jama’a.
Wannan abu ya sanya sanata mai wakiltar Zamfara a majalisar dattawa, Kabiru Marafa, yayi kira ga majalisan kan sanya dokar ta baci a jihar domin kawo karshen wannan abu.
KU KARANTA: Orji Kalu ya mayar wa da Obasanjo martani mai zafi
Jiya Laraba hukumar sojin saman Najeriya ta tura runduna na musamman domin ganin cewa an kawo karshen wadannan maras imanin da suka addabi rayuwar jama’a.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a: https://facebook.com/naijcomhausa https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng