Hukumar yan sanda ta kamo makamai 948 a jihar Sokoto

Hukumar yan sanda ta kamo makamai 948 a jihar Sokoto

Hukumar yan sandan jihar Sokoto ta bayyana cewa ta kama bindigogi 948 karkashin shirin tallafi da kuma ayyukan da yan sanda suka yi cikin watanni 24 da suka gabata.

Kwamishinan yan sanda na jihar, Mista Murtala Mani ya bayyana hakan a taron manema labarai a Sokoto a ranar Larba, 4 ga watan Afrilu.

Mani yace makaman da aka kwato da wanda suka saduda sun hada da AK47 da kuma bindigogin gargajiya 1,200.

Kwamishinan yace wasu sun mika bindigogin nasu ne a lokacin shirin tallafi wanda aka shirya domin wanzar da zaman lafiya a jihar.

Hukumar yan sanda ta kamo makamai 948 a jihar Sokoto

Hukumar yan sanda ta kamo makamai 948 a jihar Sokoto

Ya kuma kara da cewa an kwato wasu bindigogin ne a lokacin musayar wuta tsakanin jami’an hukumar da yan ta’adda.

KU KARANTA KUMA: Jihar Kaduna na bukatar $95bn domin ta gyara ayyukan cigaba - El-Rufai

Daga karshe ya jaddada cewa ana kan daukar duk matakan da suka dace domin hukunta dukannin masu kera makamai.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel