Rundunar sojin Najeriya sun ragargaji yan bindiga 21 a jihar Zamfara

Rundunar sojin Najeriya sun ragargaji yan bindiga 21 a jihar Zamfara

Kwana daya bayan hukumar sojin saman Najeriya ta tura sabon runduna ta musamman domin kawo karshen kashe-kashen da ke faruwa a jihar Zamfara, jami’an soji sun yi batakashi da yan bindigan a cikin daji.

Rundunar sojin sun yi arangama da yan bindigan ne yayinda suke shiga lungo da sako domin bankado mabuyar yan bindigan.

Sun hallaka wasu daga cikinsu kuma sun smau nasarar kwamto muggan makamai. Kakakin hukumar, Brigadier General Texas Chukwu ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya saki da safen nan.

Rundunar sojin Najeriya sun ragargaji yan bindiga 21 a jihar Zamfara
Rundunar sojin Najeriya sun ragargaji yan bindiga 21 a jihar Zamfara

Yace: “Rundunar sojin 232 Battalion Zuru yayinda suka shara ranan Laraba, 4 ga watan Afrilu 2018 sunyi arangama da yan bindiga a Tunga Daji, karamar hukumar Anka na jihar Zamfara.

Bayan artabu da akayi, wasu daga cikin yan bindigan sun tsira da raunuka. An kwato makamai irinsu AK47 5, carbin harsasai 5, da kuma harsasi masu fadin 7,62mm guda 35.

Abin takaici mun yi rashin soji 2 kuma na kai gawawwakinsu babban asibitin Gusau.”

“Kana rundunar da aka tura Bena sun kai farmaki wa yan bindiga a kauyen Laka da ke jihar Kebbi inda suka kashe guda daya kuma sun samo bindigar AK47 da carbin harsasai.”

KU KARANTA: Babban bankin Najeriya CBN ya gargadi Shugaba Buhari

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa yan bindiga masu satan shanu sun addabi al’umman jihar Zamfara a kwanakin nan. A ranan Alhamis da ya gabata, an kashe mutane da dama a kauyen Bawar Daji ba gaira ba dalili.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng