Nigerian news All categories All tags
Yanzu-yanzu: An hallaka mutane 5 a garin TY Danjuma

Yanzu-yanzu: An hallaka mutane 5 a garin TY Danjuma

Wasu mutane da ake zargin makiyaya ne sun hallaka yan gida daya 5 a kauyen Mbiya, karamar hukumar Takum na jihar Taraba, garinsu janar TY Danjuma.

Wannan abu na faruwa ne bayan Janar din ya yi kira ga al’umman Najeriya su dauki makami domin kare kansu daga makasa tunda gwamnati ta gaza.

Janar Theophilus Danjuma, tsohon ministan tsaro ne kuma babba hafsan sojin Najeriya .

Yanzu-yanzu: An hallaka mutane 5 a garin TY Danjuma

Yanzu-yanzu: An hallaka mutane 5 a garin TY Danjuma

Maharan sun babbaka uban gidan, Sunday Sabo, da ransa.

Wani idon shaida Samson Tinton, ya bayyana cewa akalla makiyaya 20 ne suka kawo farmaki kauyen a yau Laraba.

KU KARANTA: Buhari ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan Sanata Mustapha Bukar

Kakakin hukumar yan sandan jihar, David Misal ya tabbatar wanann labara amma bai yi ta’aliki ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba: https://facebook.com/naijcomhausa da https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel