An gwabza kazamin fada tsakanin sojoji da tsageran daji a Zamfara

An gwabza kazamin fada tsakanin sojoji da tsageran daji a Zamfara

Labarin da muke samu daga majiya mai tushe na tabbatar mana da cewa akalla dakarun rundunar sojin Najeriya biyu ne suka rasu a kauyen Bawar Daji na karamar hukumar Anka ta jihar Zamfara biyo bayan artabun su da 'yan bindiga.

Mun samu wadannan alkaluma ne dai daga bakin shugaban karamar hukumar ta Anka Alhaji Mustapha Gado wanda kuma ya tabbatar mana da cewa sojin sun samu nasarar kashe wasu 'yan bindigar da dama suma.

An gwabza kazamin fada tsakanin sojoji da tsageran daji a Zamfara
An gwabza kazamin fada tsakanin sojoji da tsageran daji a Zamfara

KU KARANTA: Aina'u Ade ta ayyana ranar auren ta

A wani labarin kuma, Gwamnan jihar Zamfara dake a shiyyar Arewa maso yammacin kasar Alhaji Abdulaziz Yari ya bayar da umurni ga jami'an tsaron kasar musamman ma wadanda suke a jihar sa inda ake ta kashe-kashe cewar su harbe dukkan wani farar hula da suka gani rike da makami.

Haka ma Gwamnan ya kara da cewa su ma dukkan masu garkuwa da mutane ko kuma masu bayar da wurin boye su su ma a kashe su da agan su ba tare da wata-wata ba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng