Yadda 'yan siyasa da suka ci kudin makamai ta hannun Dasuki, su 15 kacal
-
-
-
A shekarar 2015 ne kungiyar yaqi da almundahana ta gayyaci tsohon mai bada shawara akan tsaro na kasa kanal Sambo Dasuki domin ansa wasu muhimman tambayoyi akan barnatar da $2.1 da aka ware don makamai, babu wanda zai yi tsammanin sunayen wasu daga cikin manyan jiga jigan yan siyasa daga baya zai shiga cikin wannan abin kunya.
An bayyana cewa, kudin da aka ware domin siyan makamai ma sojojin da ke yaqi da ta'addanci a arewa maso kudancin kasar wasu manyan yan'siyasa suka raba kuma sukayi yaqin neman zabe dasu.
A sakamakon haka ne ta'addanci ya qara samun gurin zama duk da koken da sojojin sukayi na rashin makamai.
DUBA WANNAN: Yadda Abacha ya rasu a 1998
Yan'siyasar najeriya ya fito fili ta yanda suka sadaukar da rayukan yan'kasar sakamakon cin hanci ta yanda suka raba $2.1 biliyan tsakaninsu.
A shekaru shida da suka shude na tsananin kashe kashen rayuka sakamakon ta'addancin Boko Haram, yan'najeriya na mamakin yanda yakin ya tsawaita da kuma yanda yan'ta'addan suka mamaye jihohi har uku na kasar bayan da an san sojojin najeriya na daya daga cikin mafi inganci a duniya.
Tunda tsohon mai bada shawara a harkokin tsaro ya fara fara bayyana manyan yan siyasa da hannu dumu dumu a barnatar da kudin makaman.
1. Goodluck Jonathan
2. Olu Falae
3. Namadi Sambo
4. Toni Anenih
5. Jafaru Isa
6. Raymond Dokpesi
7. Bode George
8. Peter Odili
9. Bafarawa Attahiru
10. Bashir Yuguda
11. Rashidi Ladoja
12. Olisa Metuh
13. Jim Nwobodo
14. Adamu Mu'azu
15. Muhammed Bello Halliru
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng