Dambarwar siyasa: Hassadar Sanata Marafa ba zatai komai ga Gwamnatin zamfara ba

Dambarwar siyasa: Hassadar Sanata Marafa ba zatai komai ga Gwamnatin zamfara ba

Gwamnatin jihar Zamfara ta nuna bacin ranta da takardan da Sanata Kabir Marafa ya gabatar gaban majalisan dattawa na sanya dokar ta baci a jihar Zamfara.

Da alama dai kudirin da Sanata mai wakiltar Zamfara ta tsakiya, Kabir Marafa ya kai majalisar dattijai na bukatar sanya dokar ta baci a jihar Zamfara sakamakon yawaitar tabarbarewar matsalar tsaro, bai yiwa gwamnatin Jihar dadi ba.

Hakan kuwa ya bayyana ne a martani cikin kakkausar murya da gwamnatin Jihar ta mayar masa, ta bakin kwamishinan yada labarai da al’adu da yawon bude idanu, Alhaji Sanda Muhammad Danjari Kwatarkwashi, inda yace, tsantsar mugunta da hassada ne a zuciyar Sanatan.

Dambarwar siyasa: Hassadar Sanata Marafa ba zatai komai ga Gwamnatin zamfara ba!
Dambarwar siyasa: Hassadar Sanata Marafa ba zatai komai ga Gwamnatin zamfara ba!

Sanata Marafan dai ya mika kudirin bukatar tsige gwamnan ne daga kujerarsa sakamakon matsalar rashin tsaro da ke kara kamari a Jihar ta Zamfara, a cewarsa ya kamata ayi kamar yadda tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo yayi na tsige gwamnan Jihar Plateau Joshua Dariye don samar da zaman lafiya.

KU KARANTA: Budurwa ta kashe kanta a Jigawa

Kwamishinan ya ce,

“Har yanzu mun rasa menene burin Sanata Marafa ban a cewa a sanya dokar ta baci a Zamfara ba, amma ai ba shi da hijabi da Gwamna Abdulaziz Yari, mai yasa bai je ya bashi shawara ba”

Shi da ko ta’aziyya baije wa iyalan wadanda abin ya ritsa da su ba.

Dambarwar siyasa: Hassadar Sanata Marafa ba zatai komai ga Gwamnatin zamfara ba!
Dambarwar siyasa: Hassadar Sanata Marafa ba zatai komai ga Gwamnatin zamfara ba!

Bayan faruwar iftila’in baya-bayan nan a kauyen Bawar Daji, Gwamna Yari ba bawa jami’an tsaro umarnin harbe duk wani wanda suka kama da bindiga nan take, a matakan da Gwamnan yake dauka a yunkurinsa na farfadosa da tsaro a Jihar.” A cewar Alhaji Danjari.

Danjari ya kuma ce, “Kawai dai abinda zamu iya cewa ya zuwa yanzu shi ne, “Mugun fata ne da bakar mugunta da kuma hassada Sanata Marafa ke yiwa Gwamna Yari, wanda kuma yake kainuwa dashen Allah domin shi Allah ya zaba a matsayin gwamnan Jihar, shi kuma Marafa ba ya farin ciki da hakan. Sai ya bari domin al’ummar Jihar na jiransa ya dawo 2019 don ya auna farin jininsa.”

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng