Nigerian news All categories All tags
Sabo da kaza baya hana a yankata: Wani Kare ya yi kaca kaca da Uwardakinsa da danta

Sabo da kaza baya hana a yankata: Wani Kare ya yi kaca kaca da Uwardakinsa da danta

- Wani mahaukacin Kare ya kashe Iyayen gidansa a Jamus

- Kwararrun masu binciken kwakwaf sun dukufa don tabbatar da yadda lamarin ya faru.

Wata Mata da danta sun gamu da ajalinsu a hannun Karensu, bayan ya kai musu farmaki sa’annan ya yi fatafata da namansu, a ranar Laraba, 4 ga watan Afrilu, inji rahoton Daily Nigeria.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito jami’an hukumar kwana kwana ne suka gani gawarwakin mamatan a gidansu dake birnin Hanover a Arewacin kasar Jamus, wadanda suka tabbatar da musabbabin mutuwarsu.

KU KARANTA: Halin mutum jarinsa: Dalilai 3 da zasu baiwa El-Rufai nasara a burinsa na Tazarce a Kaduna

“Binciken farko farko ya tabbatar da cewar Karen gidan ne ya kashe Matar mai shekaru 52, da danta mai shekaru 27, yarsu mai shekaru 25 ce ta kira hukumar, bayan ta kwashe kwanaki biyu bata samu iyayen nata a waya ba.” Inji su.

Diyar matarce ta gano gawar da kanta a ranar da take gidan, inda ta hangi gawarwakin nasu kwance ta cikin taga. Sai dai kwararrun masu binciken kwakwaf sun dukufa don tabbatar da yadda lamarin ya faru.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel