2019: Adawar da IBB da Obasanjo ke nunawa ba siyasa bace
- Tsohon shugaban kasa na mulkin Soja Ibrahim Badamasi Babangida da abokinsa Obasanjo sun bayyana ra’ayoyinsu game da zaben 2019
- Babangida ya shawarci shugaba Buhari akan ya janye bukatarsa ta tsayawa takara a zaben 2019, don ya bawa matasa damar kabar jagorancin kasar
- Obasanjo kuma yay a bayyana nasa ra’ayin akan gwamnatin Buhari, inda ya nuna cewa tana tafiyar hawainiyar a fannin gudanar da ayyuka
Tsohon shugaban kasa na mulkin Soja Ibrahim Badamasi Babangida da abokinsa Obasanjo sun bayyana ra’ayoyinsu game da zaben 2019.
Babangida ya shawarci shugaba Buhari akan ya janye bukatarsa ta tsayawa takara a zaben 2019, don ya bawa matasa damar kabar jagorancin kasar, duk da cewa bayanan Janar Babangida suna nuna kishin kasa ne kawai.
Obasanjo kuma yay a bayyana nasa ra’ayin akan gwamnatin Buhari, inda ya nuna cewa tana tafiyar hawainiyar a fannin gudanar da ayyuka, saboda haka sun dage akan cewa sai buhari ya sauka mulki idan wa’adinsa ya cika.
KU KARANTA KUMA: Fadar shugaban kasa tayi umurnin sakin jerin sunayen barayin gwamnati
Dokar kasa ta 1999 ta shimfida dokoki game da duk wani dan takara dakeso ya tsaya takara ta kowane matsayi hadda na shugaban kasa. Saboda haka ba siyasa bace ka fito fili kana hana wani ya tsaya takara.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng