Fadar shugaban kasa tayi umurnin sakin jerin sunayen barayin gwamnati
- A kokarin da PDP keyi na karyata cewa shuwaganninsu sun saci biliyoyin kudi kafin zaben 2015, an bayar da umurni daga Ofishin shugaban kasa na fitar da jerin sunayen wadanda suka saci kudi
- An bayar da Umurnin ne a kashen satin nan ga hukumar kula da tattalin arzikin kasa data fitar da jerin sunayen
- Shugaban kasar yanaso ya tabbatarwa ‘yan Najeriya cewa gwamnatin adawa data shude ta debi manya manyan kudade daga taskar gwamnatin
A kokarin da PDP keyi na karyata cewa shuwaganninsu sun saci biliyoyin kudi kafin zaben 2015, an bayar da umurni daga Ofishin shugaban kasa na fitar da jerin sunayen wadanda take zargi sun saci kudin gwamnati.
Wani daga cikin ma’aikatan Ofishin shugaban kasa yace, An bayar da Umurnin ne a kashen satin nan ga hukumar kula da tattalin arzikin kasa (EFCC) data fitar da jerin sunayen.
Ofishin shugaban kasar naso ta bayyana irin ta’addancin da ‘yan adawar suka aikatawa Najeriya da ‘yan Najeriya.
Shugaban kasar yanaso ya tabbatarwa ‘yan Najeriya cewa gwamnatin adawa data shude ta debi manya manyan kudade daga taskar gwamnatin, wand aba abu bane da zasu jinginashi da kabilanci ba kamar yanda suke kokarin yi.
KU KARANTA KUMA: Obasanjo bai cancanci ya zargi kowa ba akan cin hanci da rashawa - Ayo Adebanjo
Ministan Labarai Lai Mohammed, bayan fitar da jerin sunayen a ranar juma’a da Litinin, yace ba’a fitarda jerin sunayen ba saida aka samu kwakwarar shaida akansu.
Ya kara da cewa wannan gwamnatin bazata huta ba har taga cewa duk wadanda suka saci kudaden an hukuntasu.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng