Zaben Kananan hukumomi: Rikici na neman barkewa a jam'iyyar APC ta jihar Nasarawa
Yayin da shirye-shire ke ta dada kara kankama game da zabukan kananan hukumomin jihar Nasarawa dake a shiyyar Arewa ta tsakiya a wata mai kamawa, da alamu kawunan masu ruwa da tsakin jam'iyyar APC mai mulki a jihar sun rabu.
Mun samu dai cewa jiga-jigan jam'iyyar ta APC a jihar dai tuni suka kai kukan su gaban gwamnan jihar inda suka roke shi da ya duba girman Allah kar ya kakaba masu shugabannin da ba su so a kananan hukumomin na su.
KU KARANTA: An ce Sanatoci da 'yan majalisar wakilai su maido kudaden da suke ansa na haram
Legit.ng ta samu cewa dai tuni gwamnatin jihar ta ayyana ranar 26 ga watan Mayu mai kamawa a matsayin ranar da za ta gudanar da zabukan kananan hukumomi da kansilolin jihar.
A wani labarin kuma, Wasu matasa a jihar Kaduna da suka ce suna rajin kare talaka da kuma matukar damuwa da jihar a karkashin inuwar kungiyar Kaduna Concerned Citizens ta ayyana cewa 'ya'yan ta tuni suka fara shire-shiren yi wa 'yan majalisar dattawan jihar kiranye.
Kamar dai yadda suka bayyana cewa sun fara hakan ne sakamakon korafe-korafe da kuma goyon bayan da suka samu daga al'ummar jihar musamman ma dai ganin cewa Sanatocin a cewar su ba su kaunar jihar ko kadan musamman ma ganin yadda suka hakan jihar cin bashin $ miliyan 350 daga bankin duniya.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng