Kuma! Yan Boko Haram sun hallaka soji 5
Akalla sojin kasar Kamaru guda biyar sun rasa rayukansu a wani harin da yan Boko Haram suka kai arewacin kasan.
Wannan abu ya faru da daren jiya Litinin, 3 ga watan Afrilu 2018 a kauyen Sagme, kusa da iyakan Najeriya da tekun Chadi. Game da cewar mazauna garin, wasu soji 3 sun jikkata.
Har yanzu dai babu wanda ya dau alhakin wannan hari amma ana kyautata zaton Boko Haram ne.
Zaku tuna cewa gwamnatin Kamaru, Chadi da Nijar sun hada karfi da karfe tare da sojin Najeriya domin kawo karshen Boko Haram amma har ila yau, Kaman abu ya gagara.
Tun shekarar 2014, kungiyar yan ta’addan sun hallaka akalla mutane 20,000 a Kamaru.
Jaridar Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa akalla mutane 18 ne suka rasa rayukansu a wani mumunan harin da Boko Haram ta kai barikin soji a jihar Borno wannan mako.
KU KARANTA: Na fi kaunar mutanen da za su faɗa min gaskiya komai ɗacinta– Masari ga hadimansa
Jami'an tsaro sun samu damar kashe yan kunar bakin wake 7 da sukayi niyyar tada bam da kuma wasu yan Boko Haram da suka dumfari barikin sojin.
Rahoton ya kara da cewa mutane da dama sun jikkata kuma an garzaya da su asibiti domin jinya.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng