Leke da bincike cikin wayan miji ko mata na iya janyo shiga kurkukun shekara 1 da taran $133, 000, sabuwar doka a Saudiyya
Leke da bincike cikin wayan maigida ko uwargida na isa sanadiyar garkaman ma’aurata shekara 1 a kurkuku da taran $13,000 a sabuwar dokar kare hakkin al’umma da gyaran dabi’a a kasar Saudiyya.
Wannan sabuwar doka ya shafi maza da mata a kasar Saudiyya, game da sanarwan ma’aikatar al’adun kasar.
Dokar tace: “Leke, bincike, ko dube-dube cikin na’urar Komfyuta ba tare da izini ba laifi ne”
Za’a ci mutum taran $13,000 ko zaman kurkuku ko kuma duka biyu.
“Shafukan sada ra’ayi da zumunta ya sanya cin mutunci ya yawaita.”
KU KARANTA: Yan sanda sun damke yan sara-suka 23 a jihar Kaduna
Hakazalika kasa mai makwabtaka da Saudiyya, Dubai, tana da irin wannan doka inda ta sanya tara $817 da kuma zaman kurkukun watanni 3.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng