Jerin barayi: Shugaban jam'iyyar PDP ya bukaci hakuri da diyyar Naira biliyan 1.5 daga Lai Muhammad

Jerin barayi: Shugaban jam'iyyar PDP ya bukaci hakuri da diyyar Naira biliyan 1.5 daga Lai Muhammad

Shugaban jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP), mai suna Prince Uche Secondus ya fadawa babban ministan yada labarai da kuma habaka al'adu na gwamnatin tarayyar Najeriya Alhaji Lai Mohammed cewar ya shiraya jiran sammacin kotu.

Haka ma dai mun samu cewa Shugaban na jam'iyyar PDP ya bukaci ban hakuri tare kuma da diyyar makudan kudaden da suka kai Naira biliyan 1.5 daga Lai Muhammad.

Jerin barayi: Shugaban jam'iyyar PDP ya bukaci hakuri da diyyar Naira biliyan 1.5 daga Lai Muhammad
Jerin barayi: Shugaban jam'iyyar PDP ya bukaci hakuri da diyyar Naira biliyan 1.5 daga Lai Muhammad

KU KARANTA: Yan shia na da cikakken iko a kasar Saudiyya

Uche Secondus ya bayyana cewa ko shakka babu ba zai bar kazafin da yayi masa ba na cewa ya wawuri kudin al'ummar Najeriya da suka kai Naira miliyan 200 ya tafi a banza ba.

Legit.ng dai ta samu cewa a jiya ne gwamnatin ta tarayya ta fitar da sunayen wasu jiga-jigan jam'iyyar adawa ta PDP inda suka ce sune suka wawure dukiyar 'yan Najeriya.

Haka ma dai mun samu cewa a wani labarin kuma, Ministan Labarai da Al’adun gargajiya, Lai Muhammed yace, gwamnatin tarayya ta APC bazata daina misali da kurakuren gwamnatin adawa data shude ba, saboda tanaso ta magance sake aukuwar irin wadannan kurakuran a gaba.

Babban Mai bawa shugaban kasa shawara, Femi Adesina, yace gwamnatin Buhari ta magance duk matsalolin tattalin arzikin kasar nan, saboda yanzu tana da kudade a asusun ajiyarta na waje wanda bata taba tara kamarsu ba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng