Allah buwayi: Wani matashi ya kashe katon kifi mai ban al'ajabi jinsin dorinar ruwa a Najeriya
- Allah buwayi: Wani matashi ya kashe katon kifi mai ban al'ajabi jinsin dorinar ruwa a Najeriya
- Ikon Allah: Hotunan wani katon kifi jinsin giwar ruwa da aka kama a Najeriya
Wani mutum da ba'a tabbatar da suna ko garin da yake ba a karamar hukumar Ibeno ta jihar Akwa Ibom dake a shiyyar kudu-maso-kudancin kasar nan ya kashe tare kuma da yada hotunan wani irin katon kifi mai ban al'ajabi jinsin giwar ruwa a Najeriya.
Haka ma dai a kwanan baya ne dai muka samu cewa wani jarumin mafarauci ya kashe wata giwa a kauyen Idanre na jihar Ondo dake a shiyyar kudu maso yammacin kasar nan inda shi ma ya yayata hotunan.
Legit.ng dai ta samu cewa tuni wasu 'yan Najeriyar suka fara nuna rashin jin dadin su game da yadda ake neman karar da hallittun daji masu matukar ban al'ajabi kuma gwamnati tayi kunnen uwar shegu da hakan.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng