Kurunkus: Allah ya tona asirin wata barauniya mai suna Grace mai amfani da hijabi da nikabi
Allah ya tona asirin wata budurwa mai amfani da hijabi har da nikabi wajen satan dukiyan jama’a a yankin kudu maso yammacin Najeriya.
An damke budurwar mai suna Grace ne a garin Kisi, karamar hukumar Irepo na jihar Oyo.
Jaridar Legit.ng ta samu wannan rahoto ne ta wani matashi mai suna Oluwatoyin Aliu wanda ya yada wannan labara a shafin ra’ayi da sada zumuntarsa na Facebook.
KU KARANTA: Tsohon Shugaba Obasanjo ya kara yin kaca-kaca da Gwamnatin Buhari (Bidiyo)
Matashin ya mika godiyarsa ga Allah da ya tona asirin wannan budurwa saboda da irinsu ake amfani wajen bata addinin Islama alhali ba mabiyan addinin bane.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng