Yadda hukumar SSS ta fanso yan matan Daphi da babban kwamandan Boko Haram da ya kai harin Bam a masallacin Kano
Rahotanni sun bayyana yadda hukumar yan sandan leken asiri wato State Security Service, SSS, sun yi musanyan fursuna da bangaren Al-Barnawi na Boko Haram domin sako yan matan Dapchi.
Fursunan da hukumar SSS ta saki shine babban kwamanda, Hussaini Maitagaran wanda shine ya jagoranci harin Bam da aka kai masallaci a jihar Kano wanda ya hallaka masu ibada 1000.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta bada rahoton cewa a wani jawabi da aka saki ranan 9 ga watan Satumba 2017, hukumar SSS ta alanta damke Hussaini Maitangaran.
Amma a wani jawabin Ann Mcgregor, wanda kwararren jami’in leken asiri na duniya da aka saki a jaridar News Plus ya bayyana yadda yan Najeriya da wasu yan kasashen wajen suka amfana da cinikayya da yan ta’adda.
“Tun 2009, gwamnatin Swizalan ta kware wajen aikin sulhu da diflomasiyya a rikice-rikice a nahiyar Afrika.
“Kana ana biyansu la’ada kan wannan sulhu, amma wanda ya fi batawa gwamnatocin Turai da Amurka rai shine irin sulhun da akayi wajen sakin yan matan Dapchi 105.”
“Jami’in leken asirin kasar Swizalan da Mustapha Zannah da Aisha Wakil sun taka rawar gani wajen biyan yan Boko Haram €5million euro da sakin kwandojin Boko Haram karkashin jagorancin Mr Lawal Daura.”
“Babban bayani shine sakin Hussaini Maitagaran wanda shine ya jagoranci harin Bam da aka kai masallaci a jihar Kano wanda ya hallaka masu ibada 1000.” Ann ya bayyana.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng