Kuma dai: Sai ran Hausawa 120 ya salwanta idan aka kashe Bafulatani 1 – Wasu yan bindiga sun yi wa gwamnati raddi

Kuma dai: Sai ran Hausawa 120 ya salwanta idan aka kashe Bafulatani 1 – Wasu yan bindiga sun yi wa gwamnati raddi

Wasu yan baranda sun fito da wani sabon faifan bidiyo inda suke ikirarin cewa duk lokacin da aka kashe Bafullace daya, sai sun kashe Hausawa 120 madadinsa.

Wani mai Magana da Bidiyon mai suna, Dan Gonnawa, ya ce suna da masu liken asiri da ke basu rahotanni kan matakai da take-taken jami’an tsaron Najeriya.

Dan Gonnawa ya yi ikirarin cewa sun mallaki manyan makamai kuma duk inda aka kashe Bafullatani a kasan nan, sai sun fanshe da rayukan Hausawa 120.

Kuma dai: Sai ran Hausawa 120 ya salwanta idan aka kashe Bafulatani 1 – Wasu yan bindiga sun yi wa gwamnati raddi
Kuma dai: Sai ran Hausawa 120 ya salwanta idan aka kashe Bafulatani 1 – Wasu yan bindiga sun yi wa gwamnati raddi

Ya kara da cewa suna za su iya kai mumunan hari garin Gusau, babban birnin jihar Zamfara ba tare da wani tsoro ko fargaba.

Da alamun an saki wannan bidiyo ne a matsayin martini ga gwamnatin jihar bias da umurnin da da ta baiwa jami’an tsaro kan kashe-kashen da ke faruwa a jihar.

KU KARANTA: Rikici ya barke tsakanin Hausawa da Yarbawa a Ilori

Zaku tuna cewa Jaridar Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa gwamnan jihar Zamfara, AbdulAziz Yari, ya bada umurnin cewa a harbe duk wanda aka gani da bindiga a jihar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng