Da dumi-dumi: Rikici ya barke tsakanin Hausawa da Yarbawa a Ilori

Da dumi-dumi: Rikici ya barke tsakanin Hausawa da Yarbawa a Ilori

Akalla mutane 5 sun jikkata a garin Ilori, babban birnin jihar Kwara sanadiyar wani rikici da ya barke tsakanin matasan Hausawa da Yarbawa a unguwan Sango, jiya Lahadi, 1 ga watan Afrilu, 2018.

An tattaro cewa rikici ya fara ne da daren Asabar yayinda wasu matasan Hausawa ya gwan-gwan suka far ma wani bayarabe saboda ya hanasu tsintan gwan-gwan a harabarsa.

Wannan abu ya sanya matasan Yarabawa suka suka farwa Hausawa a jiya inda wasu suka ji raunuka daban-daban.

Da dumi-dumi: Rikici ya barke tsakanin Hausawa da Yarbawa a Ilori
Da dumi-dumi: Rikici ya barke tsakanin Hausawa da Yarbawa a Ilori

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Ajayi Okasanmi, ya tabbatar da wannan labara inda yace: “Rikicin ya fara ne ranan Asabar sanadiyar rashin jituwa tsakanin matasan Hausawa da Yarbawa wanda ya sabbaba fada.”

KU KARANTA: An damke dan barandan karshe mai wa Dino Melaye aiki da ya tsere daga kurkuku

Ya ce an tura jami’an tsaron NSCDC da na yan sanda domin kwantar da kuran.

Ya kara da cewa an damke mutane 7 kuma an kai wadanda suka jikkata asibiti. Mutane 5 na hannun yan sanda kuma ana gudanar da bincike a kansu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng