Tsare-tsare game da yanda akeso a dakatar da Magu daga aiki sun bayyana
- Takaddam tsakanin jami’an gwamnati da majalisar zartarwa a kan shugaban hukumar kula da tattalin arzikin kasa bata kare ba
- Tsare-tsare game da yanda akeso a dakatar da shugaban hukumar mai rukon kwarya Ibrahim Magu, sun fito ne daga wadanda basa goyon baya akan yanda yake gudanar da aiki
- Masu goyon bayansa kuma sun bayyana cewa shine wanda yafi cancanta daya gudanar da wanannan aiki
Takaddam tsakanin jami’an gwamnati da majalisar zartarwa a kan shugaban hukumar kula da tattalin arzikin kasa bata kare ba ta yanda wanannan bangere naso a cireshi wadannan kuma naso a tabbatar dashi a wannan matsayi.
Tare-tsare game da yanda akeso a dakatar da shugaban hukumar mai rukon kwarya Ibrahim Magu, sun fito ne daga wadanda basa goyon akan yanda yake gudanar da aiki.
Masu goyon bayansa kuma sun bayyana cewa shine wanda yafi cancanta daya gudanar da wanannan aiki.
Sunce tinda magana tana kotu game da majalisar zartarwa sai ta tabbatar dashi ko kuwa ba saita tabbatar ba zai iya cigaba, ya kamata a bari babbar kotu ka yanke wannan hukunci.
Yan majalissa sun tubure a kan canzashi, ita kuma fadar shugaban kasa ta dage akan sai an tabbatar dashi bisa ga irin jajircewarsa a bincike daya gudanar, a shekaru uku da suka gabata.
KU KARANTA KUMA: Duk wanda ke korafi kan yunwa yaje ya nemi aikinyi - Hadimin Buhari
Hakan ya biyo bayan fargaba da suke dashi na cewa koda Buhari bai koma kan kujerarsa ta shugaban kasa ba idan Magu ya cigaba da rike wannan matsayi zai cigaba da bincikensu.
Sakamakon haka neman mafita suka gana a satin daya gabata ta yanda zasu dakatar dashi, bisa ga wasu dalilai da suke zarginsa akansu, musamman a cewarsu zai kawo tangarda ga zake zabar Muhammadu Buhari.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng