Jami’an Soji sun kama wasu gagaruman ‘yan ta’adda a jihar Taraba

Jami’an Soji sun kama wasu gagaruman ‘yan ta’adda a jihar Taraba

- Jami’an Soji dake gudanar da aikin bincike na Ayem Akpatuma, a jihar taraba tare da jami’an ‘Yan Sanda sunyi nasarar kama wasu ‘yan ta’adda dake ta’addanci a garin Mayo Ndaga

- Jami’an sunyi nasarar samun wasu kayayyaki a hannun ‘yan ta’addan wanda suka hada da fallayen kwanon rufi, gado da keken dinki, da injinan bayar da wutar lantarki, da kuma bindigar kugu ta hausa

Jami’an Soji dake gudanar da aikin bincike na Ayem Akpatuma, a jihar taraba tare da jami’an ‘Yan Sanda, a ranar 31 ga watan Maris 2018, sunyi nasarar kama wasu ‘yan ta’adda dake ta’addanci a garin Mayo Ndaga, inda aka samesu da fallayen kwanon rufi, gado da kuma bindigar kugu ta hausa.

Jami’an sunyi nasarar kama wasu ‘yan ta’addan, Palat Jafainal mai shekaru 20, da Kingsiley Benson mai shekaru 25, inda suma aka samesu da kayayyaki wanda suka hada da fallayen kwanon rufi, da keken dinki, da injinan bayar da wutar lantarki.

Jami’an Soji sun kama wasu gagaruman ‘yan ta’adda a jihar Taraba
Jami’an Soji sun kama wasu gagaruman ‘yan ta’adda a jihar Taraba

KU KARANTA KUMA: Zaben Gwamna: Kayode Fayemi ya zari takobin komawa kujerar sa

Sai wani Rapheal Abel da shekara 26 da Yusuf Abdulkareem, ‘yan kabilar Kaka suma an kamasu da fallayen kwano na rufi.

Jami’an Soji sun kama wasu gagaruman ‘yan ta’adda a jihar Taraba
Jami’an Soji sun kama wasu gagaruman ‘yan ta’adda a jihar Taraba

Burgediya Janar Texas Chukwu, Daraktan hurda da jama’a na Soji ya bukataci cewa duk wanda ya samu wannan muhimmin labari da ya yadawa al’umma ta hanyar sadarwa da yake dashi.

Jami’an Soji sun kama wasu gagaruman ‘yan ta’adda a jihar Taraba
Jami’an Soji sun kama wasu gagaruman ‘yan ta’adda a jihar Taraba

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng