Tsaro: Barayi da masu garkuwa da mutane 750 sun tuba

Tsaro: Barayi da masu garkuwa da mutane 750 sun tuba

- Barayi da masu garkuwa da mutane 750 sun tuba a jihar Kaduna

- Jihar Kaduna na daga cikin jihohin da ke fama da yawaitar barayi da yan garkuwa da mutane

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN), ya rawaito cewa sati uku da ya gabata ne Mutane 400 daga cikin masu aikata manyan laifuka suka tuba. tubabbun dai sun rantse ne da alkur'ani mai girma kan cewa ba za su kara cigaba da aika mummunar tsohuwar sana'ar tasu ba, yayin da a jiya Lahadi kuma karin wasu 350 suka saba tasu rantsuwar kauracewa aikin laifukan da suke aikatawa. Tuban nasu dai ya biyo bayan tattaunawa mai zurfi da shugabannin yankin suka yi da su.

KU KARANTA: Kamata yayi Najeriya ta halarta amfani da kwayoyi da basu da illa, kamar su wiwi

Tubabbun dai sun yi amfani da damar da tsarin afuwa ga wadanda suke da niyyar daina aikata laifuka da gwamnatin Jihar ta Kaduna ta bullo da shi. A cewar babban sifeton yan sanda na kasa Ibrahim Idris, duk wadanda suka tuban zasu mika makamansu ga hukuma kamar yadda tsarin ya tanadar.

Kana ya kara da cewa, ba zasu nuna makaman ga al'umma ba, sakamakon haka yarjejeniyar shirin afuwar ya tanadar, domin tubabbun su sami nutsuwa ko hakan ya bawa sauran kwarin gwuiwar mika wuya.

A jihar Kaduna barayi da masu garkuwa da mutane 750 sun tuba
A jihar Kaduna barayi da masu garkuwa da mutane 750 sun tuba

"Ina mai tabbatar muku da cewa, nan da lokaci kadan zamu karbo makaman nasu, don a yanzu ma wasu daga cikinsu sun miko mana nasu da kansu." A cewar babban sifeton

Ibrahim Idris ya kara da cewa, "Mutukar ana son magance aikata laifuka, zama tilas ai aiki tare da wadanda suke aikata laifin. Kuma sun gano cewa, masu laifin na fitowa ne daga can cikin dajin yankin, su tsorata jama'a kana su yashe su ko garkuwa da su. A dalilin haka ne suke amfani da shugannin yankin don cimma kudirin shirin afuwar."

Shugaban yan sintiri na yankin Malam Audu Sallau, ya yabawa jami;an tsaro bisa wannan gagarumar nasara, in da ya ce, "Babu daya daga cikin tubabbun da aka tilastawa tuban, hasali ma da su ne suka yanke shawarar yin hakan da kansu."

Kuma tun bayan bullo da shirin yankin nasu yake zaune lafiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel