Yanzu-yanzu: FG ta sake sakin sunayen barayin gwamnati lokacin PDP

Yanzu-yanzu: FG ta sake sakin sunayen barayin gwamnati lokacin PDP

Gwamnatin tarayya ta sake fitar da sabon jerin wadanda sukayiwa arzikin Najeriya cin zomo ga harawa tare da yawan kudaden da kowannenu ya wawura.

Yayinda ya ke sakin wannan sabon jeri, ministan yada labari da al'adu, Alhaji Lai Mohammed ya ce mutane basu gane dalilin da ya sa basu saki dukkan sunayen a karo a farko ba cewa jerin farko somin tabi ne kawai.

Duba sabon jerin sunayen mutanen da Ministan ya bayyana da adadin kudin da suka sata:

1. Tsohon NSA Sambo Dasuki: $2.1bn, N126 billion, $1.5 billion, Fam 5.5 miliyan

2. Tsohon ministan man fetur Diezani Alison-Madueke: N23bn, $3 billion

3. Laftanan Janar Kenneth Minimah: N13.9 billion

4. Laftana Janar Azubuike Iejirika: N4.5 billion

5. Tsohon shugaban soji, Alex Barde: N8billion

6. Tsohon shugaban Kwastam, Dikko Inde: N40 billion

7. Air Marshal Adesola Amosun: N21.4 billion

8. Tsohon ministan FCT, Sanata Bala Abdulkadir: N5 billion

9. Sanata Stella Oduah: N9.8 billion

10. Tsohon gwamnan Neja, Babangida Aliyu: N1.6 billion

11. Tsohon gwamnan jihar Flato, Jonah Jang: N12.5 billion

12. Tsohon karamin ministan kudi, Bashir Yuguda: N1.5 billion, $829,800

13. Sanata Peter Nwaboshi: N1.5billion

14. Aliyu Usman: N512 million

15. Tsohon gwamnan jihar Oyo, Rashid Ladoja: N500 million

16. Tomi Ikimi: N300 million

17. Femi Fani-Kayode: N866 million

18.Hassan Tukur: $1.7 million

19. Nenadi Usman N1.5 billion

20. Benedicta Iroha: 1.7 Billion

21. Aliyu Usman Jawaz: N882 million

Gabanin yanzu, gwamnatin tarayya ta saki jerin sunayen wasu manyan jigogin PDP da suka wawuri dukiyan Najeriya.

1) Shugaban jam'iyyar PDP, Uche Secondus: Ya karbi miliyan 200 ranar 19 ga watan Fabrairun 2015 daga ofishin tsohon mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkar tsaro (NSA).

2) Tsohon sakataren kudin jam'iyyar PDP: A ranar 24 ga watan Oktoba, 2014, ya karbi miliyan N600m daga ofishin tsohon mai bawa shugaban kasa a kan harkar tsaro.

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta fitar da sunayen wadanda suka saci kudin gwamnati lokacin mulkin PDP

3) Tsohon sakataren yada labaran jam'iyyar PDP, Olisah Metuh: Ana tuhumar sa da karbar biliyan N1.4bn daga ofishin tsohon NSA.

4) Dakta Raymond Dokpesi: Shugaban kamfanin DAAR; mai gidan talabijin na AIT da gidan Radiyon Ray Power. Ana tuhumar sa da karbar biliyan 2.1 daga ofishin tsohon NSA.

5) Tsohon mai bawa tsohon shugaban kasa Jonathan shawara, Dudafa Waripamo-Owei: An gurfanar da shi bisa boye kudi miliyan N830m a asusu daban-daban.

6) Robert Azibaola: Dan uwa ga Jonathan: An gurfanar da shi gaban kotu ranar Alhamis bisa tuhumar karbar Dala biliyan $40m daga ofishin NSA

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng