Soyayya ruwan zuma: Hotunan Fatima Dangote na sheke ayar ta da angon ta a bakin ruwa
- Ko shakka babu soyayya kamar yadda Hausawa ke cewa ruwan zuma ce
- Fatima Dangote tuni har sun fita yawon shakatawa ita da mijin ta a bakin ruwa
- An gudanar da bikin auren su ne a cikin watan da ya gabata
Ko shakka babu soyayya kamar yadda Hausawa ke cewa ruwan zuma ce, idan ka sha sai ka ba masoyi domin kuwa diyar shahararren mai kudin nan na daya a Afrika watau Fatima Dangote tuni har sun fita yawon shakatawa ita da mijin ta a bakin ruwa.
KU KARANTA: Sabbin kayatattun hotunan Rahama Sadau
Wannan dai mun samu hakan ne biyo bayan wasu hotuna cike da annashuwa da ma'auratan suka saki a bakin ruwa rike da hannayen junan su suna ta wasa irin na masoya.
Legit.ng ta samu cewa idan mai karatu mai manta ba ma'auratan dai sun gudanar da bikin auren su ne a cikin watan da ya gabata inda aka gudanar da kayattacen bikin kece raini.
Haka ma dai bikin ya samu halarar dukkan wasu masu fada aji a Najeriya kama daga 'yan siyasa, 'yan kasuwa, da ma sauran masu sarautun gargajiya da masu mulki.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng