Kare kai: Daga karshe, Shugaban kasa ya maidawa TY Danjuma martani

Kare kai: Daga karshe, Shugaban kasa ya maidawa TY Danjuma martani

Fadar shugaban kasar Najeriya a ranar Asabar din da ta gabata ta fitar da sanarwa tana mai maida martani ga tsohon babban jami'in rundunar sojojin Najeriya kuma tsohon ministan tsaron kasar nan watau Laftanal Janar Theophilus Yakubu Danjuma (Mai ritaya) da yayi a satin da ya shude.

Idan dai ba'a manta ba Laftanal Janar Theophilus Yakubu Danjuma (Mai ritaya) a baya ya yi kira ga dukkan al'ummar kasar nan da su tashi tsaye wajen kare kansu da kansu idan har aka zo kawo masu hari domin a cewar sa jami'an tsaron Najeriya sun gaza ta wannan fannin.

Kare kai: Daga karshe, Shugaban kasa ya maidawa TY Danjuma martani

Kare kai: Daga karshe, Shugaban kasa ya maidawa TY Danjuma martani

KU KARANTA: Mutum 3 ke neman kujerar Oyegun

To sai dai a sanarwar daga fadar shugaban kasa wadda mai taimaka masa na musamman Malam Garba Shehu ya fitar ya bayyana cewa babban abun takaici ne kalaman na sa musamman ma ganin cewa hakan zai iya tunzura jama'a su dauki makami.

A wani labarin kuma, Wani babban malamin addinin Kirista a Najeriya kuma shugaban darikar Katolika na shiyyar Sokoto Bishof Matthew Hassan Kuka ya shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta tabbatar da cika alkawurran da ya daukar wa 'yan Najeriya lokacin yakin neman zabe.

Haka ma dai Bishof din ya kuma roki sauran 'yan Najeriya musamman ma masu fada a ji da su yi anfani da damar su wajen samarwa kasar tabbataccen zaman lafiya tare kuma gudun duniya da son tara dukiya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel