Yadda tsaffin gwamnonin PDP suka ba Buhari Naira miliyan 500 na kamfen a 2014 - Bafarawa
Tsohon gwamnan jihar Sokoto na farko a wannan jamhuriyar kuma jigo a jam'iyyar PDP a jihar yanzu haka watau Alhaji Attahiru Bafarawa ya yi ikirarin cewa tsaffin gwamnonin nan na jam'iyyar PDP da suka sauya sheka ya zuwa APC a shekarar 2014 sun baiwa sabuwar jam'iyyar ta su kudin kamfen na Naira miliyan 500.
A cewar sa, kafin jam'iyyar ta APC ta amince da dawowar su tare kuma da mallaka masu ragamar jam'iyyar jihohin nasu a hannun su sai da aka umurce su da kowa ya bayar da Naira miliyan 100.
KU KARANTA: Mutum 3 da ake sa ran za su gaji Oyegun a APC
Legit.ng ta samu cewa Alhaji Bafarawa din yayi wannan ikirarin ne a yayin da yayi wata kebantacciyar fira da majiyar mu ta kamfanin jaridar Punch a karshen satin nan.
Mai karatu dai zai iya tuna cewa wadanda suka sauya shekar a wancen lokacin sun hada da Murtala Nyako (Adamawa), Abdulfattah Ahmed (Kwara) Rotimi Amaechi (Rivers), Rabiu Kwankwaso (Kano), da kuma Aliyu Wamakko (Sokoto).
A wani labarin kuma, Tsohon gwamnan jihar Kuros Ribas dake a kudu maso kudancin Najeriya na farko a wannan jamhuriyar, Mista Donald Duke a ranar Alhamis din da ta gabata ya yi ikirarin cewa asarar da Najeriya ta tafka sakamakon fadan Boko Haram ya fi wadda ta yi a lokacin yakin basasa.
Mista Duke dai ya yi wannan ikirarin ne a yayin zantawa da manema labarai a garin Legas, karkashin inuwar wata kungiya da ke rajin tabbatar da shugaba mai inganci a Najeriya watau National Movement for Positive Change (NMPC).
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng