Nigerian news All categories All tags
Rayuwar kunci ta mata-maza da 'yan daudu a Najeriya

Rayuwar kunci ta mata-maza da 'yan daudu a Najeriya

- Mata-maza dai suna faruwa a kowacce al'umma, kuma sukan sha tsangwama kan halittarsu

- Wasu har aure sukan rasa, ko a kore su daga gida

- Wasunsu sukan balaga da jinsi biyu

Rayuwar kunci ta mata-maza da 'yan daudu a Najeriya

Rayuwar kunci ta mata-maza da 'yan daudu a Najeriya

A kasar nan, ana samun mata-maza da 'yan daudu, amma kunya da rashin ilimi basu bari a tattauna matsalarsu, ko ma a taimaka musu a likitance.

Sukan sha tsangwama musamman tsakanin jama'a muddin aka ga kamar suna biye wa shigar wani jinsin da ake tsammani ba nasu ba.

A wasu addinan ma, an tsine wa dukkan wadanda suke shiga ba ta jinsin su ba, wannan yazo ne saboda addinin a zamanin da can, bai mma fahimci yadda halittar take ba, ko ma me yasa wasu ke shiga ta mata ko yanayi na mata.

DUBA WANNAN: Ashe Kwamishiniya da ta ajje aiki a Kano tana da kunzugu a banki

Gwamnati ya kamata ta taimakawa irin wadannan mutane ne domin su samu cikakkiyar rayuwa wadda babu tsangwama ko fitsara a ciki,

A kimiyyance dai, namiji yana da Chromosomes na alelles XY ne, mace kuma tana da XX, kwayoyin halitta dake ada wa jiki ko mace ne shi ko namiji. Sai dai akasin da akan samu a wasu jariran sai a sami XXY ko XYY wanda ke maida su mace da namiji a hade.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel