Nigerian news All categories All tags
Mai kamfanin facebook ya shiga uku kan zargin sace bayanai na jama'a da sayarwa

Mai kamfanin facebook ya shiga uku kan zargin sace bayanai na jama'a da sayarwa

- Mark Zuckeberg na fuskantar matsin kotu kan saba dokar adana bayanai

- An gano yana sayar da bayanan mutane ga kamfunna da suke neman sirrikan mutane

- Ya karyata batun cewa ya karya doka

Mai kamfanin facebook ya shiga uku kan zargin sace bayanai na jama'a da sayarwa

Mai kamfanin facebook ya shiga uku kan zargin sace bayanai na jama'a da sayarwa

Mark Zuckerberg, biloniyan saurayi da ya kafa kamfanin facebook, ya fara fuskantar binciken majalisu da kotuna a Amurka da Birtaniya, saboda ganowa da akayi ashe facebook din yana nadar bayanan mutane kan rayuwarsu ya sayar wa wasu kamfunnan.

Zuckerberg, ya karyata cewa ya karya wata dokar sirrin jama'a ko aikata ba daidai ba, duk da cewa kamfanin da ya zuki bayanai ya esar don samun kudi ko lada.

An kiyasta cewa, muddin kakin hau facebook da wayarka/ki, to kuwa manhajar ta nadi dukkan sirrika da bayanai da ke kan wayar, wadanda ba ma su shafi facebook din ba, kamar su lambobin waya, kudi a banki, sakonni da ma soyayya.

DUBA WANNAN: Saudiyya ta nesanta kanta da Izala

A Amurka dai ana ta rufe shain saboda tsoron ko ya keta dokar sirrin mutane ko kuma a'a, wasu kuwa sunce basu damu ba.

Akwai akalla mutum biliyan biyu a duniya dake amani da shafi da manhajar facbook don samun labaru da hirar gulma.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel