Jerin barayi: Shugaban jam'iyyar PDP ya sha alwashin maka Lai Muhammad kotu
Shugaban jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP), mai suna Prince Uche Secondus ya fadawa babban ministan yada labarai da kuma habaka al'adu na gwamnatin tarayyar Najeriya Alhaji Lai Mohammed cewar ya shiraya jiran sammacin kotu.
Uche Secondus ya bayyana cewa ko shakka babu ba zai bar kazafin da yayi masa ba na cewa ya wawuri kudin al'ummar Najeriya da suka kai Naira miliyan 200 ya tafi a banza ba.
KU KARANTA: Tuni 'yan Najeriya suka yafe mana - PDP
Legit.ng dai ta samu cewa a jiya ne gwamnatin ta tarayya ta fitar da sunayen wasu jiga-jigan jam'iyyar adawa ta PDP inda suka ce sune suka wawure dukiyar 'yan Najeriya.
A wani labarin kuma, Jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta bayyana jerin mutanen da gwamnatin APC ta wallafa da sunan cewa barayi ne a matsayin karya da soki-burutsu tsagwaron sa.
Haka zalika jam'iyyar ta PDP ta kuma bayyana cewa an zayyana sunayen wasu daga cikin jiga-jigan ta ne kawai domin a bata masu suna duk kuwa da cewa wasu daga cikin su duk maganar su na a gaban kotu.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng