Da dumin sa: Jami'an 'yan sanda sun cafke wanda ya yi wa dalibar jami'ar Maiduguri wanka da guba
Kamar dai yadda muka samu, jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya shiyyar jihar Borno dake a Arewa maso gabashin kasar nan a ranar Alhamis din da ta gabata ne ta tabbatar da samun nasarar cafke wani matashi mai suna Musa Faisal bisa samun sa da hannu dumu-dumu a watsawa tsohuwar budurwarsa, guba.
Budurwar ta sa mai suna Fatima Usman mai shekaru 26 a duniya dai mun samu cewa a kwanan baya an same ta kwance jina-jina kafin a garzaya da ita asibiti sakamakon wankan da ake zargin yayi mata da ruwan guba.
KU KARANTA: PDP ba za ta taba dawowa mulki ba - Tinubu
Legit.ng dai ta samu cewa tsohon saurayin nata dai ya bayyana cewa ya watsa mata gubar ne saboda iyayenta sun hana shi aurenta duk kuwa da irin tsawon lokacin da suka shafe suna soyayya.
Fatima Usman dai take matakin karshe a fannin lafiya a jami'a Maiduguri an watsa mata ruwan guban ne a ranar 16 ga watan Maris, 2018. Inda guban ya shafi fuskar ta da wasu sassa na jikinta.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng