Hukumar ‘Yan Sanda a jihar Edo ta kama wasu mutane 5 da makamai 120
- Hukumar ‘Yan Sanda a kokarin da takeyi na kawar da amfani da makamai a fadin kasar nan kayi nasarar gano wasu makamai 120
- Kwamishina ‘Yan Sanda Johnson Kokumo, ya bayyana hakane a ranar Laraba, lokacin da yake zantawa da manema labarai
- Kokumo yace, an samu bindigogi AK-47 guda 9, sai Halba ruga guda 15, sai kanan bindigogi na gargajiya guda 61, sai bindigar kugu ta hausa da ta turawa 25, sai G-3 guda 1, sai TO6 guda 1, sai K2 1, sai barreta guda 1, kananan bindigogi guda biyu
Hukumar ‘Yan Sanda a kokarin da takeyi na kawar da amfani da makamai a fadin kasar nan kayi nasarar gano wasu makamai 120, hakan ya biyo bayan umurnin shugaban hukumar ‘Yan Sandan na kasa.
Kwamishina ‘Yan Sanda Johnson Kokumo, ya bayyana hakane a ranar Laraba, lokacin da yake zantawa da manema labarai, a Benin.
Kokumo yace, an samu bindigogi AK-47 guda 9, sai Halba ruga guda 15, sai kanan bindigogi na gargajiya guda 61, sai bindigar kugu ta hausa da ta turawa 25, sai G-3 guda 1, sai TO6 guda 1, sai K2 1, sai barreta guda 1, pistol guda biyu.
Ya kara da cewa hukumar ta gano akwatin harsasai 154 sannan kuma an kama mutane biyar a cikin aikin da aka gudanar tsawon watannan.
Haka kuma jami’an su kama wasu mutane uku da ake zargin ‘yan kungiyar masu garkuwa da mutane.
KU KARANTA KUMA: An nemi masoyan Shugaba Buhari su lissafo aikin da Gwamnatin nan ta iya kammalawa cikin shekaru 3
Kwamishinan ya bayyana cewa ‘yan ta’addan sunyi barazanar sace wani mai suna Reuben, idan har bai biya N1m cikin asusun ajiyarsu na banki ba.
Ya kuma yi godiya ga mutanen garin bisa ga hadin kai da suka bayar ta hanyar bada muhimman bayanai akan ‘yan ta’addan.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng