Yan bindiga sun kashe makiyaya 15 a jihar Zamfara
- Wasu ‘yan bindiga dake zargin barayin shanu ne sun kashe wasu makiyaya 15 a wani sabon tashin hankali dake faruwa a Arewacin Najeriya
- ‘Yan ta’addan sun kai hari a kauyen Bawon-Daji inda suka hallaka mutane 15 a ciki
- Ma’aikacin karamar hukuma a jihar, Gado Anka, ya bayyana cewa ‘yan ta’addan sun shiga kauyen ne akan Babura
A ranar Alhamis hukumar ‘Yan Sanda da kuma dattawan kauye sun bayyana cewa, wasu ‘yan bindiga dake zargin barayin shanu ne sun kashe wasu makiyaya 15 a wani sabon tashin hankali dake faruwa a Arewacin Najeriya, a kauyukan makiyaya.
'Yan ta’addan sun kai hari jiya, a kauyen Bawon-Daji inda suka hallaka mutane 15 a ciki”, mai magana da yawun hukumar ta ‘Yan Sanda a jihar Zamfara, Muhammad Shehu, ya bayyanawa AFP.
Ma’aikacin karamar hukuma a jihar, Gado Anka, ya bayyanawa AFP, cewa ‘yan ta’addan sun shiga kauyen na Anka ne saman Babura da misalign karfe 1 na rana, inda suke harbe mutane 12 har lahira kafin su gudu zuwa cikin daji.
KU KARANTA KUMA: An mayar da shari’a dake tsakanina da ‘Yan Sanda birnin tarayya - Dino Melaye
“Bayan awowi biyu suka dawo, suka kara kawowa mutane hari a cikin makabarta, inda suka kara hallaka mutane 3, suka kuma raunata dayawa a ciki”, inji shi.
Kauyuka a yankin suna cikin tashin hankali na ‘yan ta’addamasu kashe mutane har cikin gidajensu. Wanda hakan ya sanya ‘yan kauye suka hada kungiyar masu kula da gari, wadanda yanzu ake zargin suna kashe barayi ba kan ka’ida ba, wanda hakan ke harzuka ‘yan ta’addan sun kara kai hari a kauyukan.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng