Shugaban Kiristocin Duniya Fafaroma ya karyata samuwar wutar Azaba a lahira
Shugaban Kiristocin Duniya, Fafaroma Francis ya musanta samuwar wutar azaba a lahira, inda yace babu wata wuta da aka tanadar ma masu laifi a lahira, inji rahoton Daily Trust.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Fafaroma ya bayyana haka ne cikin wata hira da yayi da jarida, inda yace: “Bayan mutuwa, wadanda suka yi ma Ubangiji biyayya zasu shiga rahama, wadanda suka baude kuwa, kuma basu nemi gafara ba, basu da gafara a ranar, sai dai a batar da su, irin bacewar layar zana.”
KU KARANAT: Kuma dai: Cikin awanni 24 Yan bindiga sun kai hari wani kauye sau biyu, sun kashe 25
Don haka Fafaroman ya tabbatar da cewar: “Samuwar wutar azaba ba gaskiya bane, abinda ke tabbatacce shi ne ruhin masu laif zai bace bat!” kamar yadda ya shaida ma wani shahararren mutumi da bai yadd da addini ba, Euginio Scalfari.
Sai dai dama a baya an sha samun maganganu masu tsauri daga wajen wannan dan jarida, wadanda yake dangantasu ga Fafaroman, sai dai fadar ta Vatican bata tanka ire iren rahotannin ba.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng