An mayar da shari’a dake tsakanina da ‘Yan Sanda birnin tarayya - Dino Melaye

An mayar da shari’a dake tsakanina da ‘Yan Sanda birnin tarayya - Dino Melaye

- Sanata Dino Melaye lamarin tsakaninsa da hukumar ‘Yan Sanda an mayar dashi Birnin Tarayya

- An zargi Sanatan na jihar Kogi, da bayar da bayanan karyaga ‘Yan Sandan a dangane da ikirarin da yakeyi na yiwa rayuwarsa barazana

- Hukumar ‘Yan Sandan ta baza sunansa a cikin wadanda Hukumar ‘Yan Sanda ke nema

Sanata Dino Milaye, mai wakiltar Kogi ta Yamma a majalisar wakilai, yayi ikirarin cewa lamarin dake tsakinsa da shugaban hukumar ‘Yan Sanda na Lokoja, an mayar dashi birnin tarayya daga garin Lokoja, dake jihar Kogi.

Ya bayyan hakan ne a shafinsa na yanar gizo na tuwita, a ranar Laraba, 28 ga watan Maris.

Yace, “ba jimawa Lauya na Ricky Tafa, ya bayyana mani cewa lamarin dake tsakanina da shugaban hukumar ‘Yan Sanda na Lokoja an mayar dashi kotun dake tarayya dake birnin tarayya, Allah abun godiya ne” ya rubuta.

A ranar Laraba 28 ga watan Maris, ne hukumar ‘Yan Sanda ta saka neman Melaye tare da Mohammed Audu, yaron tsohon Gwamnan jihar ta Kogi, Abubakar Audu.

An mayar da shari’a dake tsakanina da ‘Yan Sanda birnin tarayya - Dino Melaye

An mayar da shari’a dake tsakanina da ‘Yan Sanda birnin tarayya - Dino Melaye

Legit.ng ta ruwaito cewa hukumar ‘Yan Sanda na Kogi sun tabbatar da cewa mutane biyun da ake zargi Sanatan na basu makamai don tayar da hankali a jihar kogi gabanin zuwan zabe na 2019, sun gudu.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya kai ziyarar kwanaki 2 jihar Lagas

Kwamishinan ‘Yan Sandan, Ali Janga, a ranar Laraba 28 ga watan Maris, ya bayyana guduwar wadanda ake zargin tare da wasu mutane suma ake zargi su hudu. Janga ya bayyana guduwarsu daga Division ‘A’ a Lokoja, da misalign karfe 3:20 na daren Laraba, 28 ga watan Maris.

Legit.ng ta ruwaito cewa Melaye lokacin da yake jawabi a majalisa a ranar Laraba 28, ga watan Maris, ya gabatar da doka ta 43 wadda yace hukumar ‘Yan Sandan sun sai wadanda ake zargin ko kuma sun kashesu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel