Tsohuwa mai shekara 100 ta musulunta a Abuja
- Tsohuwa yar shekara 100 ta karbi addinin musulunci a babban birnin tarayya
- An shafe shekaru da dama ana yi mata tayin Musulunci sai yanzu Allah ya bata ikon karban addinin
- A cewarta ta kan ji dadi idan aka ambaci Annabi Muhammadu tun kafin musuluntar ta
Wata tsohuwa mai shekaru 100 da haihuwa a yankin Karshi dake babban birnin tarayya Abuja ta karbi addinin Musulunci.
An kwashe tsawon shekaru da dama yaýa da jikoki na yiwa wannan tsohuwa tayin addinin Musulunci amma abun ya ci tura sai a yanzu ne Allah ya bata ikon karbar wannan addini.
Ta musulunta ne a sanadiyan wani maulidi da aka shirya na auren daya daga cikin jikokinta.
Sheikh Adamu Inuwa wanda shine babban limamin garin Karshi dake birnin tarayya ya ce, akwai lokacin da ta tara 'ya'yantagargade su cewa duk wanda ya kara cewa ta shiga musulunci zata tsine masa, wannan yasa suke jin shakkar kiran ta zuwa musulunci, amman ni duk da haka ban gaji da zuwa wajanta ba don da'awah.
KU KARANTA KUMA: Atiku ya bukaci magoya bayansa da suyi katin zabe kafin 2019
Wani abin mamaki ga ita wannan baiwar Allah duk sanda ake Mauludin Manzon Allah SAW ko mu Zahara sai ta fito, har ma tana fadin duk sanda ta ji an ambaci Manzon Allah SAW takan samu nutsuwa a zuciyar ta.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng